Min menu

Pages

latest news

Hisbah ta sa kyautar Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya fallasa inda za'a samu Abdul Babulaye

 Hisbah ta sa kyautar Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya fallasa inda za'a samu Abdul Babulaye

👇👇👇



Hoton Bidiyon da  yasa hukumar Hisba ke neman Abdul Babulaye ruwa a jallo


Janairu 10, 2023 

Wata majiya daga hukumar Hisba na cewa jami'an tsaron hukumar sun baza komar su don nemo Jarumin film Abdul Babulaye domin ya amsa tambayoyi game da irin bidiyoyin da yake wallafa wa a shafukansa na sada zumunta na zamani wato Social Media.


Ana zargin Abdul Babulaye da wuce gona da iri wajen yada bidiyon barkwanci wadanda ake ganin basu dace da addini da kuma al'adar malam bahaushe ba, ana nuno Abdul Babulaye rungune da yan mata a wani lokacin suna yin kalamai wadanda sam basu dace ba.


Sai dai har yanzu babu wani karin bayani daya fito daga wanda ake zargin.


A wani labarin kuma.


Gwamnatin Jihar Yobe ta bada hutun ranaku 2 domin zuwan mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari


Gwamnatin jihar Yobe ta sanya ranakun yau Litinin da gobe Talata a matsayin hutu domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.


Shugaban ma'aikata na jihar, Garba Bilal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu.


Shugaba Buhari zai ziyarci jihar ne domin kaddamar da wasu ayyuka da su ka hada da filin jirgin sama na jiragen kaya, kasuwar zamani da kuma cibiyar kula da lafiyar mata da yara.

A cewar Bilal, Gwamna Mai Mala Buni ya ayyana ranar hutun ne domin baiwa ma'aikatan gwamnati da sauran jama'a damar tarbar shugaban da zai kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar.


"Na rubuta ne domin sanar da ku cewa mai girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya ayyana ranakun Litinin 9 da Talata 10 ga Janairu, 2023 a matsayin ranakun hutu," in ji sanarwar.


"Wannan shine don baiwa ma'aikatan gwamnati da sauran jama'a damar tarbar shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, wanda zai ziyarci jihar domin ziyarar aiki ta kwana daya."


Ya bayyana cewa ma'aikatan gwamnati za su koma bakin aiki a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu.


Comments